in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mayakan Boko Haram sun yi saranda da makamansu
2014-09-22 10:40:52 cri

Hukumomi a Nigeria sun ba da tabbacin cewar, wasu daga cikin 'yan ta'adda na kungiyar nan mai tada kayar baya ta Boko Haram sun fara yin saranda tare da makamansu, bisa radin kansu a sakamakon wani gagarumin farmaki da dakarun Nigeria suka kaddamar a kan 'yan kungiyar.

Hedkwatar rundunar tsaro ta Nigeria ta fada a cikin wata sanarwa wadda ta shiga hannun kamfanin dilancin labarai na Xinhua cewar, a ranar Asabar din da ta shige ne, 'yan kungiyar ta Boko Haram masu tada zaune tsaye su 5 suka yi saranda da illahirin makamansu, tare da gabatar da rokon neman ahuwa a garin Konduga na jihar Borno.

Sauran 'yan kungiyar wadanda suka ki yin saranda, amma kuma sojoji sun cafke su, su ma sun ba da muhimman bayanai a kan ajandar kungiyar, a wani yunkuri da ake gani suna kokari ne su ba da hadin kai.

A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, mayakan 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram sun sha gudanar da yunkuri dabam-daban domin samun nasara shiga garin Konduga, to amma sai sojojin Nigeria suka taka masu birki suka wargaza aniyarsu.

Hukumomin tsaron na Nigeria sun ce, dakarun Nigeria sun cafke wani babban kwamanda na kungiyar ta Boko Haram wacce ake dorawa alhakin kashe rayukan daruruwan jama'a tun daga shekara ta 2009. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China