An rantsar da firaministan kasar Libya Abdullah Thinni da majalisar ministocin shi a wani biki da aka gudanar, sai dai kuma ana hasashen cewar, wannan mataki zai haifar da ci gaba da arangama tsakanin gwamnatin Islama ta Tripoli da kuma masu marawa Thinni baya.
An gudanar da bikin rantsuwar ne a garin Tobruk, inda kuma nan ne fadar gwamnatin firaministan Thinni da 'yan majalisar dokokinsa, wadanda suka samu goyon bayan kasashen duniya, kuma sabbin nadin da Thinni ya yi ya hada da mataimakan firaminista guda 3, da kuma ministoci 10.
A ranar Litinin din da ta wuce ne majalisar dokokin kasar ta baiwa Thinni da mukarrabansa goyon baya da kwarin gwiwa da kuma ba su umurni na magance rikicin da ya addabi kasar ta Libya, da kuma kawo karshen kazamin fadan da ake tabkawa tsakanin kungiyoyi tsagera na musulmai da kuma kungiyoyi dake goyon bayan gwamnati, wacce ba ta da nasaba da addini.
Kasar ta Libya ta fada cikin rikicin siyasa tun bayan tashin hankalin da ya wancakalar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011.
Kawo ya zuwa yanzu kungiyoyi masu adawa da juna guda biyu kowannnensu ya kafa gwamnatinsa da majalisar dokokinsa. (suwaiba)




