Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya ce, babu hujjoji karara, dake tabbatar da zargin da aka yiwa tawagar UNAMID, na boye gaskiyar lamari game da halin da fararen hula ke ciki a yankin Darfur na kasar Sudan.
A ta bakin kakakinsa, sakamakon binciken da aka kammala ya nuna cewa, ko alama, babu wata hujja dake nuna aniyar tawagar wanzar da zaman lafiyar ta UNAMID, ta boye wasu laifukan cin zarafin bil'adama da ake zargin dakarun sojin kasar na yi kan fararen hula. Ko da yake a hannu guda Mr. Ban ya bayyana damuwa game da yadda tawagar ta gaza, wajen mika rahoton wasu lamura da suka faru ga helkwatar MDD.
Kaza lika rahoton binciken ya nuna yadda tawagar ta UNAMID ta yi sakaci wajen sanar wa manema labaru halin da ake ciki, game da wasu lamura da suka dace a fayyace su.
Babban magatakardar MDDr ya ce, duk da mawuyacin halin aikin da wannan tawaga ke fuskanta, bai kamata ta rufe batutuwan da suka jibanci keta hakkin bil'adama, ko wata barazana ga rayukan ma'aikatan wanzar da zaman lafiya ba.
An dai gudanar da wannan bincike ne biyowa bayan bukatar hakan daga babbar kotun hukunta manyan laifuka ta duniya a cikin watan Yunin da ya shude, kudurin da kuma ya samu amincewar kasashen Faransa da Birtaniya. (Saminu)




