Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta sanar a ranar Litinin da kisan wani jami'in diplomasiyyar kasar Spaniya a birnin Khartoum.
Jami'in dake kula da bangaren harkokin jakadanci na ofishin jakadancin Spaniya dake kasar Sudan, an iske shi ba rai, bayan an daka masa wuka a cikin gidansa dake unguwar Garden City, a tsakiyar birnin Khartoum, in ji ma'aikatar harkokin wajen a cikin wata gajeriyar sanarwa. Tuni kuma, hukumar 'yan sanda ta kaddamar bincike da neman mutanen da suka aikata wannan kisa domin gurfanar da su gaban kotu, in ji ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan, tare da jaddada cewa, tana dukufa wajen aikin tabbatar da tsaron lafiyar dukkan jami'an diplomasiyya da 'yan kasashen waje dake Sudan. (Maman Ada)




