in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi maraba da kafa hukumar wucin gadi a kudu maso yammacin Somaliya
2014-06-25 10:48:38 cri

Babban sakatare na MDD, Ban Ki-moon ya yi maraba a ranar Talata da yarjejeniyar da aka cimma dake ba da damar kafa wata sabuwar hukumar yanki ta wucin gadi a kudu maso yammacin kasar Somaliya, dake hada yankunan Bay, Bakool da Bas Shabelle.

Shugaban MDD ya jinjinawa dukkan bangarorin da suka taimaka wajen cimma wannan muhimmiyar yarjejeniya, tare kuma da nuna gamsuwarsa kan aiwatar da wannan mataki cikin sauri, in ji kakakin MDD, Stephane Dujarric a yayin taron manema labarai.

Mista Ban ya tunatar cewa, kafa wannan hukumar yankin dake tattara ko wani muhimmin matakin farko ne na shirin kafa tsarin baiwa yankunan damar gudanar da harkokin kansu a kasar Somaliya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar na wucin gadi ya tanada, da kuma tabbatar da hanyar da mutanen Somaliya suke son dauka, in ji mista Dujarric.

Haka kuma mista Ban ya jaddada niyyar MDD wajen tallafawa ayyukan wanzar da zaman lafiya da kuma kokarin gwamnatin tarayya ta Somaliya take yi wajen kafa wata jiha. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China