in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin MDD na neman taimakon dalar miliyan 186 domin 'yan gudun hijirar Afrika
2014-07-02 11:53:47 cri

Wasu hukumomi 2 na MDD sun yi kira da a tattara kudi na dalar Amurka miliyan 186, domin a taimakawa 'yan gudun hijira fiye da dubu 800 a Afrika wadanda ke fama da karamcin abinci.

Wata sanarwa ta hadin gwiwa daga hukumar samar da abinci ta MDD, da kuma hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, ta ce, a sakamakon karancin abincin da 'yan gudun hijirar ke fafutuka, hakan ya haifar da karin wasu matsaloli saboda 'yan gudun hijirar na tunkarar kalubalen ta hanyar da ba ta dace ba.

Sanarwar ta ce, hukumomin MDD. dinkin duniyar guda biyu, dole ne ya sa suka rage yawan abincin da suke baiwa 'yan gudun hijirar, saboda karancin kudi, da rashin tsaro da matsalolin da ke tasowa, wadanda ke yin barazana lalata yanayin da dama ya tabarbare, hakan ya sa yara kananan na fuskantar matsalar abinci mai gina jiki, rashin girma na yara da karancin jinni.

A halin da ake ciki, akwai 'yan gudun hijira miliyan 2.2 a wasu cibiyoyin kula da 'yan gudun hijira 200 da ke cikin kasashen Afirka 22, kuma dukanin 'yan gudun hijirar sun dogara ne a kan taimakon abinci daga hukumar samar da abinci ta MDD.

A halin da ake ciki, kashi daya bisa uku daga cikin 'yan gudun hijirar, an rage musu yawan abincin da ake ba su, kuma 'yan gudun hijira daga kasar Chadi, an rage musu kashi 60 bisa dari na abincin da ake ba su. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China