in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Sin na taka muhimmiyar rawa cikin tattalin arzikin Zimbabwe
2014-05-15 09:53:27 cri

Ministan harkokin kudi na kasar Zimbabwe Patrick Chinamasa ya ce, kamfanonin kasar Sin na taka gagarumar rawa a cikin tattalin arzikin Zimbabwe, saboda a yanzu haka, su ne ke gudanar da manyan ayyuka da kasar ke aiwatarwa.

A yayin da yake amsa tambayoyin 'yan majalisar kasar, a yayin wani zama da majalisar ta gudanar, Chinamasa ya ce, Zimbabwe da kasar Sin suna da babbar dangantaka, wadda ta sa bangarorin biyu suna hada kai wajen aiwatar da wasu manyan ayyuka, musamman a bangaren samar da wutar lantarki.

A shekarar bara, kasar Zimbabwe ta baiwa kamfanin kasar Sin mai gudanar da ayyuka na injiniya, kwangila na fadada tashar wutar lantarki ta Hwange a kan kudi, har dalar Amurka biliyan 1.3, hakazalika, kamfanin kasar Sin, Sino Hydro, shi kuma an ba shi kwangilar dalar Amurka miliyan 355, domin kamfanin ya fadada tashar samar da wutar lantarki ta kudancin Kariba. Ana sa ran cewar, ayyukan guda biyu, za su samar da karin karfin wutar lantarki a Zimbabwe har ya kai Megawatts 900. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China