Da misalin karfe 8 sauran minti 23 na ranar 20 ga wata da safe, kasar Sin ta samu nasarar harba wata roka, dake dauke da taurarin dan Adam na gwajin fasahohi da kimiyya zuwa sararin samaniya. Yanzu wadannan taurarin dan Adam guda 3 sun riga sun shiga hanyoyinsu da aka tsara cikin sararin samaniya.
An labarta cewa, za a yi amfani da wadannan taurarin dan Adam guda uku wajen gwajin binciken buraguzan dake cikin sararin samaniya, da kuma yin gwajin amfani da hannun injuna wajen gyara na'urorin dake tafiya cikin sararin samaniya. (Sanusi Chen)