Hukumar tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana cewa, harin da Amurka ta kai ta sama ranar Litinin kasar Somalia, ta kai ne da nufin halaka shugaban mayakan kungiyar Al-Shabaab da aka tsegunta mata cewa, yana sansanin kungiyar a wannan lokaci.
Sakataren hulda da 'yan jarida na hukumar ta Pentagon John Kirby ya ce, sojojin Amurka na musamman sun kai harin ne kan sansanin mayakan kungiyar ta Al-Shabaab ta hanyar mafani da jirage masu matuka da kuma marasa matuka, musamman da nufin halaka shugaban kungiyar Ahmed Abdi al-Muhammad, wanda aka fi sani da suna Ahmed Godane.
Ya ce, an kai harin ne bayan da hukumar ta Pentagon ta samu bayanan asiri da ke nuna cewa, Godane yana sansanin kungiyar da ke kudancin Mogadishu, babban birnin kasar Somalia.
Ko da yake Kirby ya ce, babu wani bayani game da ko an kashe Godane ko a'a, sakamakon harin na sama da sojojin Amurka suka kaddamar. Ya ce, ana tantance sakamakon harin da Amurka ta kai, kuma babu wani sojan Amurka a kasa a lokacin da sojojin nata suka kai wannan hari. (Ibrahim)