Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya yi kira da a inganta hadin gwiwa tsakanin MDD da ragowar kungiyoyi na shiyyoyin duniya daban daban a fagen shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya.
Liu wanda ya bayyana hakan a yayin zaman mahawarar da kwamitin tsaron MDDr ya gudanar a ranar Litinin, ya ce, hadin kan sassan zai taimaka matuka wajen habaka nasarorin da ake fatan cimmawa.
Zaman na jiya dai ya mai da hankali ne ga tattauna tasirin hadin gwiwar kungiyoyin shiyyoyin duniya, da alakar hakan ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.
Da yake karin haske kan wannan batu, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya bayyana cewa, tsahon shekaru, hadin gwiwar MDD da irin wadannan kungiyoyi na shiyya-shiyya kamar su kungiyar AU, ya taka muhimmiyar rawa, wajen cimma nasarar wanzar da yanayin zaman lafiya a yankuna kamar su Darfur a Sudan, da kasar Somalia, da Mali, da janhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Sudan ta Kudu.
Kwamitin tsaron MDDr dai ya sha alwashin bunkasa wannan dangantaka, tare da kira ga babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, da ya nazarci halin da ake ciki game da hakan da nufin wannan manufa. (Saminu)