Kwararru a kasar Sin sun ce, sabon tsarin habbakar birane zai zaburar da ci gaban kasar mai dorewa ya zuwa mataki na gaba.
Kwararrun sun yi jawabi ne a yayin gudanar da wani zaman taro a kan tsarin habbakar birane na kasar Sin, a jiya Litinin a babbar hedkwatar MDD.
Taron mai taken "labarin kasar Sin na 2, sabbin hanyoyin habbakar birane" ya mai da hankali a kan nasarar da za'a samu a bangaren ci gaba mai dorewa na duniya, a bisa la'akari da sabon shirin habbakar birane na Sin daga shekara ta 2014 zuwa ta 2020, shirin yana da manufar tabbatar da cewar, bunkasar biranen na kasar Sin, an yi su tare da la'akari da jin dadin jama'a da kuma kare muhalli.
Mataimakin shugaba kuma sakatare janar na kwamitin asusun makamashi na Sin CEFC, Patrick Ho Chi-Ping, ya ce, sabon tsarin habbakar biranen wani shiri ne da zai baiwa jama'ar kasar Sin damar samun kasonsu na nasarori da habbaka da aka samu domin su tafiyar da rayuwarsu cikin girmamawa da gamsuwa, ta yadda ko wane mutum zai iya gane albarkar da yake da ita, tare da kaiwa ga cimma manufofinsu na rayuwa.
Wannan kungiya mai zaman kanta CEFC, ita ce ta dauki nauyin gudanar da zaman taron. Kungiyar wacce ta kunshi kwararru, ta sadaukar da kanta wajen huldar diplomasiyya, da bincike a kan muhimman abubuwa, amma ta fi ba da karfi wajen makamashi da al'adu. A watan Maris na shekarar bara ne, kungiyar ta gudanar da zaman taro na farko mai taken "Ci gaba mai dorewa da kuma maganar mulki". (Suwaiba)