in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira da a kara la'akari kan aikin wanzar da zaman lafiya na MDD
2014-10-10 10:59:45 cri

Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi a ranar Alhamis din nan 9 ga wata ya yi kiran da a kara la'akari a kan ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.

Liu Jieyi ya yi kiran ne a lokacin taron kwamitin tsaron majalissar game da ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Ya ce, a lokacin aika jami'an wanzar da zaman lafiya, ya kamata a tabbatar da cewar, ayyukan da za'a gudanar suna bisa muradun ka'idojin majalissar, sannan a tantance takamaiman ayyukan da jami'an za su gabatar, su kuma mai da hankali a kai har ila yau su guji tattara dukkan ayyukan da wassu ba shi ne mafi mahummanci ba a lokacin wanzar da ayyukan nasu.

Wakilin na kasar Sin ya ba da shawarar a tantance sakamakon kowane aiki da aka gabatar a cikin lokaci, da kuma yadda ake bukata, ya nuna tare da sauyin da aka cimma domin a san gyaran da za'a yi a sauran ayyukan na gaba da suka hada da karfi da adadin dakarun da za'a sake aikawa kasashe masu bukata.

Ya kuma lura da cewar, ayyukan wanzar da zaman lafiya ya kamata a aiwatar da su ne kamar yadda kwamitin tsaron ya shawarta, yana mai nuni da cewa, yawan tura jami'an tsaro ba shi ne mafita ba a wuraren da ake fuskantar tashin hankali, illa tattaunawar siyasa wajen warware matsalolin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China