in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musulmai sun koma kasar Sin bayan sun kammala aikin hajji a Mekka
2014-10-28 15:16:50 cri

A karkashin shugabancin hukumar kula da harkokin addinai ta kasar Sin, ma'aikatan diflomasiyya, tsaron lafiyar al'umma, jiragen saman fasinja, binciken ingancin kayayyaki, kiwon lafiya, kwastan da dai sauransu sun hada kansu sosai, don ganin aikin hajji ya tafi lami lafiya. Sa'an nan kungiyar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Sin ta aika da tawaga mai wakilai fiye da 50, wadanda suka bai wa musulmai daga kasar Sin da suka je aikin hajjin hidimomi ta fuskar harkokin addini, kiwon lafiya, tsaron lafiya da dai makamantansu.

Dangane da halin musamman da ke akwai game da aikin hajji da aka yi a bana, Adilijiang Ajikelimu, mataimakin shugaban kungiyar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Sin ya gaya mana cewa, "Kamar yadda mu kan yi a baya, mun jagoranci maniyatan da za su je aikin hajji bisa shirin da aka tsara. Har wa yau da nufin ganin an hana yaduwar annoba, a bana mun kara ma'aikatan kiwon lafiya tare da inganta ayyukan yin rigakafi. Sa'an nan mun kara karfin ma'aikatanmu a fannonin harkokin addini da dai sauransu. A yayin da musulman kasar Sin suke yin aikin hajji bana a kasar Saudiya, sun kammala aikin hajji yadda ya kamata, haka kuma sun kyautata yin mu'amala da musulmai daga sassa daban daban na duniya yadda ya kamata. Mun jagoranci musulmai ta yadda suka yi aikin hajjin na bana yadda ya kamata."

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China