in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musulmai sun koma kasar Sin bayan sun kammala aikin hajji a Mekka
2014-10-28 15:16:50 cri

A cikin dukkan musulman da suka yi aikin hajjin bana, akwai alhazai dubu 600 da suka fito daga kasar Saudiya, sauran alhazai miliyan 1 da dubu 400 sun zo ne daga sassa daban daban na duniya, ciki had da musulman kasar Sin kusan dubu 14 da dari 5.

Kowa ya san cewa, aikin hajji na da matukar muhimmanci ga musulmai, kasancewarsa daya daga cikin shika-shikan addinin guda biyar. Don haka ya zuwa yanzu Alhazai da dama suna farin cikin kwarai yayin da suka waiwayi yadda suka yi aikin hajjin. Yang Xiuhua, wata musulma ce da ke zaune a titin Niujie a nan birnin Beijing. Ta gaya mana cewa, "Ina jin farin cikin kwarai da gaske! Ban san abin da zan iya fada ba. Lokacin da na isa MakkaMekka, Allah kadai na ke tunani a zuciya ta. Yayin da na shiga masallaci, ba a bin da na ke yi sai Allah-Allah na kusanci dakin Ka'aba. Na jin farin ciki sosai."

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China