in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musulmai sun koma kasar Sin bayan sun kammala aikin hajji a Mekka
2014-10-28 15:16:50 cri


Daga ranar 11 ga watan Oktoba na bana ne, rukuni na farko na musulman kasar Sin suka dawo gida bayan kammala aikin hajjin bana a Mekka da ke kasar Saudiya. Ya zuwa ranar 27 ga watan da muke ciki fiye da alhazai dubu 13 ne suka koma gida kasar Sin. Ranar 27 ga wata da tsakar rana, jami'an hukumar kula da harkokin addinai ta kasar Sin da kungiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar Sin suka marabci wadannan alhazai. Ranar Alhamis 30 ga wata da safe ne ake sa ran rukuni na karshe na alhazan kasar Sin za su iso Beijing ta jirgin sama . Abokiyar aikin mu Tasallah ta hada mana rahoto na musamman a kai.

Jiya Litinin 27 ga wata da tsakar rana, a filin jirgin sama na kasa da kasa da ke nan Beijing, musulmai kusan dari daya daga sassa daban daban na kasar Sin suka marabci 'yan uwa da dangoginsu da suka kammala aikin hajjin bana a Mekka da ke kasar Saudiya. Li Hongjie, wani musulmi ne daga gundumar Nanle ta lardin Henan ya gaya mana cewa, shi da sauran alhazai daga gundumarsa sun zo Beijing ne cikin wata babbar motar da suka yi haya, domin su tarbi limanin masallacinsu, wanda ya dawo daga aikin hajjin na bana."'Musulmai kimanin 30 daga gundumarmu mun zo nan rike da kyawawan furanni domin yin maraba ga limaminmu, wanda shi ne Alhaji na farko a gundumarmu ta Nanle. Saboda muhimmancinsa ya sa dukkan musulman da ke wurin ke maraba da dawowarsa.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China