Bayan wani artabu tare da sojojin kasar Tunisia a ranar Lahadi da safe a wata unguwar Al-Ouardia dake kudancin birnin Tunis, dakarun musamman na yaki da ta'addanci sun halaka wani dan kishin islama da kuma jima wani na daban a cikin wata arangama, in ji ministan cikin gidan kasar Tunisia a cikin shafinsa na Facebook.
A cewar ma'aikatar harkokin cikin gida, mutane biyu dake dauke da makamai suna cikin wani gungun miyagun 'yan ta'adda dake kunshe mambobi takwas. Sauran mambobin shida sun shiga hannun jami'an tsaro da aka jibge wurin sosai.
Gungun 'yan kishin islama ya fake ne a cikin wani gidan dake wannan unguwa dake kusa da kofar shigowa ta kudancin birnin Tunis.
Haka kuma ministan cikin gidan Tunisia ya jaddada cewa, ana cigaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin abkuwar wannan lamari tare da bayyana cewa, za'a gurfanar da wadannan mambobin kishin islama a gaban kotu. (Maman Ada)