Ministan raya kasa na cikin gidan kasar Masar Adel Labib a Litinin ya ce, farmakin da aka kai wa a arewacin Sinai ba za su dakatar da lokacin da aka tsayar ba na gudanar da zaben majalisar dokokin kasar.
Wata jaridar gwmanati da ake bugawa a kafar sadarwa ta shafin Internet Ahram, ta bayyana cewar, hare-haren da wasu rukunoni masu hadari da wasu masu tada kayar baya suka kai a Sinai suka haifar da asarar rayukan sojojin kasar a kalla 30, tare da jikkata wasu da dama. A sakamakon wadannan hare-haren, Masar ta kafa dokar ta baci a yankin Sinai.
Minista Labib ya kuma shaida wa manema labarai cewar, da zarar an kammala zaben majalisar dokokin kasar, daga nan za'a tunkari gudanar da zabuka na yankuna nan da zuwa karshen shekara.
Zaben majalisar dokokin shi ne mataki na karshe a jerin taswirar zabe wanda aka shimfida bayan da aka hambarar da gwamnatin musulunci ta tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi a Yulin shekarar 2013. (Suwaiba)