Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta baiwa kasar Ghana tallafin dalar Amurka dubu 50 domin yaki da barkewar cutar kwalera, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 100 a kasar.
Jakadan kasar Sin a Ghana, Sun Baohong wadda ta mika guddumuwar kasar Sin a hannun kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Ghana a jiya Litinin, ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da bayar da tallafi a fannin kula da kiwon lafia na kasar Ghana.
Sun ta ce, kasar Sin za ta samar da wani taimako na kayayyakin kiwon lafiya wanda darajarsu ta kai zunzurutun kudi har dalar Amurka dubu 800, ga kasar ta Ghana domin Ghanar ta samu sukunin girka matakai na tunkarar cutar Ebola.
Jakadar kasar Sin a Ghana ta yi fatan cewar, kasashen Afrika ta yamma za su samu sukunin wargaza cutar a cikin 'dan kankanin lokaci, musamman saboda tallafin da suke samu daga kasashen ketare. (Suwaiba)