Gwamnatin jihar Borno wacce ke arewa maso gabashin Nigeria ta ce, za ta fara binciken lamarin sace wasu yara 'yan mata da mata 60 da aka yi, tare da kashe wasu mutane 30 a wasu hare-hare da aka kai a garuruwan mutanen, wadanda ke cikin lungun jihar a karshen makon da ya gabata..
Kakakin gwamnatin jihar Isa Gusau, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewar, gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, ya umurci jami'ai a yankunan da aka kai hare-haren da su gudanar da cikakken bincike na gaskiya a cikin gaggawa ta hanyar tattaunawa da jama'ar wuraren da aka kai harin, tare da gabatar da rahoto na gaggawa.
Gwamnatin jihar ta Borno, wacce ke fama da kalubalen tsaro, sakamakon hare-hare na kungiyar Boko Haram, a halin da ake ciki jihar ta Borno tana daukar wannan sabon mataki na sace mata da 'yan mata a matsayin wani muhimmin lamari. (Suwaiba)