in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Brazil ta kara zabar shugaban kasar mai rike da madafun iko karo na biyu
2014-10-27 14:25:14 cri

Sakamakon kuri'un da aka kada ya nuna cewar, an sake zabar shugaban kasar Brazil madam Dilma Rousseff, 'yar shekaru 66 a karo na biyu.

Sakamakon zabe da aka bayar jiya Lahadi na nuni da cewar, shugaban kasar Rousseff ta lashe kashi 51.62 bisa dari daga cikin kashi 99.77 bisa dari na kuri'un da aka kada.

Sakamakon zaben ya kuma nuna cewar, abokin takararta 'dan jam'iyyar 'yan adawa Aecio Neves kuma ya samu kashi 48.38 bisa dari na kuri'un da aka kada.

A yayin kamfe din madam Dilma Roussef ita kuma ta yi alkawarin shimfida wani sabon ginshikin ci gaba mai dimbin yawa ga tattalin arzikin kasar.

Nasarar Dilma tana nufin shekaru hudu na rike madafun iko a hannun 'yan jam'iyyarta ta Workers wadanda suka rike mulki tsawon shekaru 12 a kasar ta Latin Amurka. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China