in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sandan Najeriya sun tsaurara matakan tsaro yayin gasar kwallon kafa ta duniya
2014-06-13 10:46:20 cri

Hukumar 'yan sandan tarayyar Najeriya a jihar Enugu, wacce ke kudu maso gabashin kasar, ta ce, ta tsaurara matakan tsaronta a cibiyoyin kallon gasar kwallon kafa a duk fadin jihar, a sakamakon fara gasar kwallon kafa ta duniya ta shekara 2014 da aka yi a Barazil.

Kakakin 'yan sandan jihar Ebere Amaraizu, ya shaidawa 'yan jarida, a Enugu, fadar gwamnatin jihar, cewar, karin sintiri da sa ido na jami'an tsaron, na da zimmar dakushe duk wani yunkuri na aikata ta'addanci da tashin hankali, wanda ka iya abkuwa a lokacin gasar kwallon kafar ta duniya.

Amaraizu ya lura da cewar, barazana da kalubale na tsaro a kasar Najeriya sun sanya dole suka hada karfi da wuraren da aka bude domin kallon wasan kwallon kafa, saboda tabbatar da kariyar masu kallon.

Ya kara da cewar, tabbatar da tsaro a wadanan cibiyoyi, ba wai abu ba ne, da ya rataya a kan wadanda suka mallaki shagunan kallon, ko kuma 'yan sanda su kadai, har ma da su masu kallon ya kamata su sa ido su ga wane ne ke zamne kusa da su a yayin da suke kallon. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China