Kasar Iran da sauran manyan kasashen duniya 6 a ranar Laraban nan suka fara wani zama na karshe domin samo mafita game da wa'adin karshe a kan batun nukiliya da aka tsai da a ranar 20 ga wannan watan da muke ciki.
A nan da makonni uku, Iran da sauran kasashen 6 da wannan batun ya shafa da suka hada da kasashen din din din guda biyar a MDD da kuma Jamus za su tattauna a kokarin samo mafita da za ta kawo karshen fito na fito da ake yi game da nukiliyar kasar ta Iran.
Ana sa ran wannan tattaunawar ta samo mafita ingantacce kafin wa'adin karshe a ranar 20 ga watan Yulin nan da aka tsai da a taron Geneva.
A watan Nuwamba na shekara 2013, kasar Iran da kasashen 6 suka cimma wata matsaya a taron Geneva, inda kasar ta dakatar da wassu ayyukanta na nukiliya, wanda a madadin hakan kuma kasashen yammaci suka dage mata wassu takunkumi na wucin gadi. (Fatimah)