in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Nigeria sun kame babban kwamandan Boko Haram
2014-09-19 13:41:54 cri

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin hukumar tsaro ta Nigeria, ta ce, kwamandan na kungiyar Boko Haram da aka kama wanda har yanzu ba'a bayyana sunansa ba, yanzu haka yana karbar magani a wata cibiyar sojoji, kuma an kama shi ne a ranar Laraba da ta gabata a wani farmaki da dakarun Nigeria suka aiwatar a kan 'yan kungiyar ta Boko Haram, mai tada zaune tsaye. Ana zargie shi da haifar da asarar rayukan daruruwan jama'a tun daga shekarar 2009.

Sanarwar ta ci gaba da cewar, adadin mayakan 'yan kungiyar Boko Haram 60, ne suka mutu a wadansu hare-hare da Boko Haram ta kaddamar da zimmar samun kafar shiga yankin garin Konduga, wanda ke jihar Borno, dake arewa maso gabashin Nigeria.

Sanarwar ofishin hukumar tsaron ta Nigeria, ta kara da cewar, dakarun Nigeria sun karbe babura guda 4 daga hannun yan ta'addan a yayin da suka yi karin batta da 'yan kungiyar ta Boko Haram a wani harin kwantan bauna a garin Benishek dake jihar ta Borno.

Sanarwar ta ce, kungiyar ta Boko Haram ta kara yin wani kokari na kai hari a garin Konduga da zagaye a jiya Alhamis, to amma sai dakarun gwamnatin Nigeria suka wargaza aniyar masu tada kayar bayan. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China