in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fada tsakanin Rwanda da DRC ya haddasa asarar rayuka 4
2014-06-12 12:43:22 cri

Fada ya barke tsakanin sojojin jamhuriyar damokradiyyar Congo DRC, da kuma dakarun 'yan adawa na Rwanda a kan iyakan nan da ake ta samun rikici jiya Laraba ran 11 ga wata, fadan ya haddasa kashe sojojin Congo guda 4, kamar dai yadda wata sanarwa ta bayyana.

Wata sanarwa daga gwamnatin Rwanda ta ce, fada da aka yi tsawon miniti 30 ana yi ya barke ne kafin safiya a garin Kanyesheze, wanda ke kilomita20 a arewacin babban birnin yankin Goma.

Sanarwar ta yi zargin cewar, fadan da ake yi na daga cikin matakan zagon kasa, da jamhuriyar damokradiyya Congo ke ci gaba da dauka, domin ta da zaune tsaye a yankin.

Sanarwar ta ce, an yi fadan ne, a gidan kurkuku na Rusura, wanda ke bangaren Busasamana, a yayin da wani bangare na sojojin jamhuriyar damokradiyyar Congo suka tsallake kan iyaka, suka shiga Rwanda, inda suka bude wuta a kan rundunar sintirin tsaro ta kasar Rwanda.

Wannan harin ya zo ne 'yan watanni kafin a cika shekara guda da 'yan Congo suka kaddamar da hari da bama-bamai a cikin kasar Rwanda.

A cikin sanarwar ministan harkokin waje na Rwanda, kuma kakakin gwamnatin Rwanda Louise Mushikiwabo ya gargadi shugabannin demokradiyyar Congo da su dakatar da duk wani hari a nan gaba. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China