Shugaban kasar Benin Boni Yayi ya gudanar da wani gyaran fuska ga gwamnatinsa da a halin yanzu take kunshe da mambobi ishirin da bakwai a tare da zuwan wani sabon ministan kudi, Komi Kountche, da baya ya rike mukamin ministan sadarwa. Wadannan sabbin nade-nade sun shafi shigowar sabbin ministoci bakwai da kuma sallamar wasu ministocin bakwai da canjawa ministoci hudu kujeru. (Maman Ada)