Amurka ta kai hari a kan makwantar 'yan kungiyar masu jihadi IS dake kamfanin Koniko mai samar da iskar gas wanda ke garin Khasham a yankin gabashin Syria na Deir al-Zour, kamfanin na da mahimmancin gaske saboda shi ne masana'anta mafi girma mai samar da iskar gas da ya koma karkashin masu tada kayar bayan a kwanan nan.
Kungiyar kare hakkin bil'adama "the Observatory" mai sa ido kan rikicin a bangaren 'yan adawa na Syria, ita ce ta bayyana hakan a hedkwatarta dake birnin London, kuma ta kara da cewar, kungiyar ta IS ta mai da wani bangare na kamafanin samar da iskar gas din a matsayin wata cibiya da take tsare jama'a, kuma harin da Amurkar ta kai jiya Lahadi ya raunata wasu 'ya'yan kungiyar masu jihadin ta IS.
Kungiyar ta ci gaba da cewar, harin da Amurkar ta kai ya fada a kan kofar shiga kamfanin Koniko mai samar da iskar gas, wanda ke ba da makamashi ga tashar rarraba hasken wutar lantarki ta Jandar, wacce ke gundumar Homs dake tsakiyar kasar, ita tashar ta Jandar tana rarraba wutar lantarkin ya zuwa tashoshin samar da wutar lantarki na daukacin kasar ta Syria, wacce yaki ya daidaita. (Suwaiba)