in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi maraba da mikawa tawagar MDD aikin wanzar da zaman lafiya a CAR
2014-09-15 14:50:01 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana farin cikinsa, game da mika ragamar aikin wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR ga tawagar MDD.

Wannan mataki dai, a cewar wata sanarwa da kakakin Mr. Ban ya fitar na shaida cewa, daga yanzu, tawagar MDDr ta MINUSCA ce za ta ci gaba da jagorantar ayyukan wanzar da zaman lafiya, wanda a baya tawagar MISCA karkashin kungiyar AU ke aiwatarwa. Lamarin da a cewar Mr. Ban zai baiwa sojoji da 'yan sandan MINUSCAn damar aiki yadda ya kamata a kasar.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai ta sha fama da rikice-rikice bisa dalilai na siyasa, inda a watan Disambar bara mayakan kungiyar musulmi ta Seleka suka rika kai hare-hare kan 'yan adawarsu, lamarin da ya yi sanadiyar kifewar gwamnatin shugaba Francois Bozize, wanda ya arce daga birnin Bangui, fadar gwamnatin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China