in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gwabza fada tsakanin bangarori biyu na Seleka a Bambari na CAR
2014-08-29 09:57:21 cri

Kimanin mutane 80 suka mutu, kana wasu kusan talatin suke jikkata a cikin bata kashi a birnin Bambari dake tsakiyar kasar Afrika ta Tsakiya CAR a ranakun Litinin da Talata tsakanin bangarori biyu na tsoffin 'yan tawayen kungiyar Seleka dake fama da rigingimun rabuwar kawuna, a cewar wani adadin wucin gadi da wasu majiyoyin hukumomi da shugabannin wannan kungiya suka fitar a ranar Alhamis.

Tsakanin dakarun janar Joseph Zoundeko, shugaban rundunar sojojin Seleka da aka zaba, tun kafuwar kungiyar a Bambari a cikin watan Mayu, da kuma mayakan Fulani dake karkashin janar Ali Djarass, karamin manjo janar dake kula da ayyukan yaki na tsoffin 'yan tawayen Seleka da aka kora tun watannin uku da suka wuce daga kan mukaminsa na komandan yankin soja na wannan birni, inda wani rikicin sanya ido kan wata tashar bincike ya sa a gwabza fada tsakanin bangarorin biyu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China