in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararriya kan hakkin dan adam za ta isa CAR
2014-09-09 10:23:11 cri

Wata kwararriya mai zaman kanta kan hakkin dan adam, madam Marie-Therese Keita Bocoum za ta fara wani rangadin aikinta karo na uku a kasar Afrika ta Tsakiya CAR daga ranar 10 zuwa 20 ga watan Satumba.

Wannan sabuwar ziyara na zuwa a daidai wani lokaci mai muhimmancin gaske wajen aiwatar da kuduri mai lamba 2149 na kwamitin tsaro na MDD, dake shirin mika ikon tawagar kasa da kasa ta wanzar da zaman lafiya a Afrika ta Tsakiya (MISCA) zuwa ga babbar tawagar kasa da kasa ta MDD domin tabbatar da zaman lafiya a Afrika ta Tsakiya (MINUSCA) a ranar 15 ga watan Satumba mai zuwa.

Daya daga cikin muradunta shi ne, na rike hankalin gamayyar kasa da kasa da kwamitin kare hakkin dan adam kan babbar matsalar da ake fuskata a CAR har zuwa lokacin da za'a cimma nagartattun hanyoyin warware wannan matsala, in ji madam Keita Bocoum.

Bayanan da za a samu a yayin wannan ziyara za su taimaka mata wajen shiryawa da gabatar da wani rahoto ga kwamitin kare hakkin dan adam na MDD a yayin zaman taronsa karo na 27, a ranar 24 ga watan Satumba mai zuwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China