in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga kasashen Afrika da su tattara arziki cikin gida domin cike gibin bukatunsu na kudi
2014-10-13 15:26:10 cri

Wajibi ne kasashen Afrika su tattara arziki cikin gida domin cike gibin bukatunsu na kudi, in ji mahalarta dandalin cigaban Afrika (ADF IX) karo na tara a birnin Marrakech na Morocco a ranar Lahadi, a cewar kafofin watsa labarai na kasar. Domin cimma wannan dama, ya kamata kasashen Afrika su bullo da nagartattun tsare-tsare na fadada gidauniyar haraji, habaka matsayin yin tsimin kudi, da kuma bunkasa kasuwannin zuba jari, ta yadda za'a janyo karin zuba jarin kai tsaye daga kasashen waje (IDE), in ji mahalartan. Haka kuma ya zama wajibi a fara kawo manyan sauye-sauye domin sanya hannu yadda ya kamata kan albarkatun da ba'a fara hakar su ba ko ba'a kula da su da kyau.

Wadannan sauye-sauye na da manufar magance matsalar karuwar hanyoyin kudi ba bisa doka ba, kafa karfin hukumomin kudi dake taimakawa kara janyo hanyoyin samun kudade na kawo sabon salo, kamar dangantaka tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP), kudaden kasa da jarin 'yan kasa dake waje. A cewar darektan dunkulewar shiyya da gine-gine a kwamitin tattalin arzikin MDD game da Afrika (UNECA), mista Stephen Karingi, dogaron Afrika kan taimakon samun bunkasuwa ba zai cigaba da kasancewa ba. Dole ne kasashen Afrika su tattara kudade domin zuba jari a bangaren masu zaman kansu, a kuma nuna cewa, ya zama wajibi Afrika ta bunkasa wani tsarin da zai taimakawa cigaban jarin masu zaman kansu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China