in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Togo ta yi kira da a yi hadin gwiwa domin yaki da rashin tsaro
2013-11-27 12:15:27 cri

Ta'addanci a yankin Sahel da kuma matsalar rashin tsaro, da ma manyan laifuffuka a mashigin tekun Guinee na bukatar ayyukan yin hadin gwiwa tsakanin shiyya shiyya, har ma tsakanin kasa da kasa, in ji ministan harkokin wajen kasar Togo, mista Robert Dussy a yayin wata ganawar musanyar ra'ayi tare da jami'an diplomasiyya na kasashen Turai dake kasar Togo.

Duk da kokarin da aka yi, shiyyar yammacin Afrika na cigaba da fuskantar kalubalen tsaro dalilin ayyukan ta'addanci dake kamari a yankin Sahel, da ma matsalar 'yan fashin teku a yankin tekun Guinee

Wannan matsala na kiran mu kara azama wajen bullo da ayyukan hadin gwiwa na shiyya shiyya da na kasa da kasa, domin yaki da wadannan bala'u dake janyo babbar illa ga kwanciyar hankali a wannan shiyya da ma zaman lafiya da tsaron kasa da kasa yadda ya kamata, in ji mista Dussy.

A watannin baya bayan nan, sojojin ruwan Togo suna daga da 'yan fashin teku kan jiragen ruwan da ke ratsa ruwan kasar Togo domin tsirar da jiragen ruwan daukan kayayyaki da na masu yawon bude ido. Haka zalika jimi'an tsaron Togo sun samu ganimar miyagun kwayoyi masu tarin yawa a tashar ruwan birnin Lome na kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China