in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijar zai kai ziyarar aiki a Benin
2014-09-02 10:04:24 cri

Shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou zai isa birnin Cotonou, babban birnin tattalin arzikin kasar Benin a ranar Laraba mai zuwa, a cikin wata ziyarar sada zumunci da aiki ta sa'o'i ishirin da hudu, a cewar wata sanarwar ta ma'aikatar harkokin wajen kasar Benin.

A cewar sanarwar, wannan ziyarar na cikin tsarin ciyar da musanya ta lokaci lokaci da shugabannin kasashen biyu ke mai da hankali a kai, da matakin karfafa huldar abokantaka da dangantaka dake tsakanin kasashen biyu, da kuma na al'ummomin kasashen biyu.

Haka zalika, ziyara wata dama ce ga shugaban kasar Benin Boni Yayi, da ya tattauna da takwaransa na Nijar, kan muhimman batutuwan da suka shafi moriyar kasashen biyu, musammun ma batun gina hanyar layin dogo na Benin-Nijar, kafa cibiyoyin bincike na kan iyaka da Malanville, da sabbin hanyoyin saukaka shige da fice a kan tashar ruwan Port de Cotonou, da ma hanyar Corridor ta Cotonou-Niamey. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China