in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da katafaren shirin yaki da zazzabin cizon sauro
2013-09-25 10:49:48 cri

A ranar Talata 24 ga watan nan ne gungun masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya, da hadin gwiwar MDD suka kaddamar da wani katafaren shirin yaki da cutar zazzabin cizon sauro, cutar da aka yi amanar na hallaka kimanin mutane 660,000 a kowace shekara.

Wannan sabon shiri wanda shirin yaki da cutar na RBM, da shirin samar da ci gaba, na MDD UNDP suka kaddamar, yayin babban taron MDD karo na 68 dake gudana a birnin New York, zai mai da hankali ne ga tsara yadda za a shigar da daukacin tsare-tsaren ci gaban rayuwar bil'adama cikin shirin yaki da wannan cuta.

Har ila yau, sabon shirin ya tanaji hanyoyin kara fadada yaki da cutar zazzabin na cizon sauro, wanda aka yi imanin cewa, yana kawo gagarumin nakasu ga ci gaban rayuwar bil'adama, musamman ma wadanda ke kasashen dake kudu da hamadar Sahara.

Bisa kididdigar da shirin samar da ci gaba na UNDP ya fitar, an ce, wannan cuta na janyowa kasashen dake Afirka asarar da ta kai dalar Amurka miliyan duba 12, ko da yake dai karin kudaden tallafi da aka sanya cikin shirye-shiryen yaki da ita, ya haifar da tarin nasarori, ciki hadda raguwar cutar da kaso 25 bisa dari a dukkanin fadin duniya.

An kuma bayyana cewa, kasashe 43 sun kai ga rage yaduwar cutar da kaso 50 bisa dari.

Tuni dai aka sanya shirin yaki da cutar zazzabin cizon sauro cikin kudurorin cimma muradun karni, a hannu guda babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya ayyana shi cikin manyan kudirorin da za su baiwa muhimmanci a zangon aikinsa na biyu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China