in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a nuna fim din Mandela a kasar Sin
2014-07-10 09:52:16 cri

A ranar 18 ga wannan wata ne ake sa ran nuna fim din nan na Mandela mai suna "Long Walk To Freedom" wato gwagwarmayar neman 'yanci don murnan tunawa da ranar Mandela ta kasa da kasa ta shekarar 2014, wadda za a yi a nan kasar Sin.

Mutumin da ya shirya fim din Anant Singh ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, za a nuna fim din a gidajen nuna fina-finai guda 1,000 da ke kasar ta Sin. Manufar nuna fim din a kasar Sin ita ce baiwa Sinawa damar sanin rayuwar Mandale, tare da nuna masa girmamawa a matsayin mutumin da ya yi suna a duniya, kana shugaban da kasar Sin ke girmamawa.

Wannan shi ne karo na farko da aka nuna wani fim din kasar Afirka ta Kudu a kasar Sin, wanda ya zo dai-dai da cikon shekaru biyu da shirin musayar al'adu tsakanin Sin da Afirka ta Kudu wanda aka kaddamar a watan Afrilu a nan birnin Beijing.

A ranar 28 ga watan Nuwamban shekarar 2013 ne aka kaddamar da fim din a kasar Afirka ta Kudu, fim din da ya kasance mafi sayuwa a tarihin fina-finai a kasar ta Afirka ta Kudu a cikin makonni biyar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China