in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Nigeriya sun tsaya kai sun san inda 'yan matan Chibok suke
2014-05-29 12:28:08 cri

Rundunar sojojin Nigeriya ta dage a kan cewa, tana sane da inda ake tsare 'yan matan sakandare na Chibok fiye da 200, da kungiyar Boko Haram ta sace a jihar Borno

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar, major janar Chris Olukolade ya shaidawa wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin Nigeriya cewa, su dai muradinsu shi ne kare rayuwar yaran dake fadawa cikin hadari.

A yayin da yake jawabi a kan hari da aka kai a kwanan nan a Buni Yadi dake jihar Yobe, Olukolade ya ba da tabbacin cewar, an kashe sojoji 12, da 'yan sanda 13, a lokacin fada da 'yan bindiga, to amma ya musanta zargin da ake yi cewar, rundunar sojojin nigeriya ta ki taimakawa sojojin na Buni Yadi, a tsawon awoyin da aka yi ana kai masu hari.

A yayin da aka tambaye shi a game da rahotanni da ke cewa, mayakan Boko Haram sun kafa tutarsu a wasu garuruwa dake jihar Borno, ya ce, rundunar sojojijn Nigeriya ba za ta amincewa wani bangare na Nigeriya ya yi amfani da wata tuta ta dabam ba domin kamar yadda ya ce, aikin sojojin Nigeriya ne su kare mutuncin kasar Nigeriya.

Olukolade ya bayyana cewa, bisa la'akari da bayanai na sirri da kuma wasu bayanai daga 'yan Nigeriya a yanzu haka an yi kame-kame a sassa dabam-dabam na jihohin dake tsakiyar arewaci na jihohin Kaduna da Zamfara. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China