Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana damuwa matuka game da wani mummunan harin da 'yan tawayen Sudan ta Kudu suka kai garin Nassir da ke jihar Upper Nile.
A cikin wata sanarwa da kakakin Ban ya bayar, ya bayyana cewa, harin na iya kara haifar da barazana ga shirin wanzar da zaman lafiyar da ke tangal-tangal.
Bayanai na nuna cewa, 'yan tawayen sun kai harin ne bisa umarnin tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Riek Machar, kuma wannan shi ne hari mafi muni tun lokacin da sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu da na 'yan tawaye suka kudurin aniyar martaba yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka sanya hannu a kai cikin watan Mayu.
Don haka Mr. Ban ya yi kira ga dukkan sassan da abin ya shafa da su gaggauta dakatar da tayar da hankali, kana su rungumi shirin sasantawa a siyasance. (Ibrahim)