in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sufurin jiragen saman Afrika na iya dunkulewa wuri guda a 2016
2014-09-25 15:20:11 cri

Kungiyar jiragen sama ta Afrika ta ce, ta yiwu nan da shekara ta 2016, kasuwar sufuri ta jiragen sama a nahiyar Afrika ta zamanto kasuwa ta bai daya, wacce za ta kawar da duk wani takunkumi na yarjejeniyar shiga sararin sama ta Afrika.

Magatakardan kungiyar Elijah Chingosho ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, ana sa rai nan da watan Oktoba ne za'a kammala tsara dokoki a game da dokar.

Wata yarjejeniya ta Yamoussoukro tun daga shekarar 1988, ta yi kira da a cire duk wani shinge yaDda jirage daga ko ina suna iya gudanar da jigila zuwa Afrika, to amma kuma tun a wancan lokacin, an kasa aiwartar da hakan saboda a kare jirage na cikin gidan Afrika daga durkushewa. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China