in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci Afrika da ta zuba jari a bangaren samar da madara
2014-09-25 15:13:48 cri

MDD ta yi kira a kan kasashen Afrika da su zuba jari a bangaren samar da madara a matsayin wani yunkuri na inganta samar da isasshen abinci.

Wani jami'in kiwon dabbobi a karkashin kungiyar abinci da harkokin noma ta MDD Olaf Thieme ya shaidawa wani taron kwanaki 3 a kan samar da madara cewar, saboda wasu matsaloli, har yanzu ba'a zuba isasshen jari a fannin kiwon dabbobi ba.

Thieme ya bukaci gwmanatocin kasashen da su hada hannu da kamfanoni masu zaman kansu domin inganta bangaren samar da madarar sha domin kamar yadda ya ce, kananan makiyayya ne ke samar da yawancin madarar da ake amfani da ita a kasashen na Afrika, kuma kamar yadda ya ce, lokaci ya yi da za'a taimakawa irin wadannan makiyayya domin su kara yawan madarar da suke samarwa.

Taron da aka yi a Nairobin Kenya ya samu halarcin wakilai 600 daga kasashe 40, wadanda suka duba sabbin fasahohi da suka shafi samar da madara.

Jami'in ya ce, a halin da ake ciki kididdiga na nuni da cewar, sauran kasashen duniya sun zarce Afrika wajen yawan madarar da suke amfani da ita, saboda haka kamar yadda ya ce, akwai bukatar daukar mataki na inganta bangaren samar da madara. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China