in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya samarwa Togo tallafin kudi dalar Amurka miliyan 14
2014-01-15 14:41:21 cri

Bankin duniya ya samar da taimakon kudi na dalar Amurka miliyan 14 ga kasar Togo a matsayin mataki na shida na tallafin kudi domin kyautata harkokin kudin kasar da muhimman sauye-sauyen cigaban tattalin arziki dake gudana a cikin wannan kasa.

An sanya hannu kan wannan yarjejeniya a ranar Talata tsakanin ministan tattalin arziki da kudi na Togo, Adji Ayassor da mista Herve Assah, wakilin bankin duniya dake kasar Togo.

Kwamitin zartarwa na bankin duniya, ya amince da wannan mataki, a karshen shekarar 2013 bisa nufin taimakawa harkokin kudi bisa adalci cikin kasar, bunkasa tsarin tattalin arziki mai kyau da kuma karfafa gishiken cigaban tattalin arziki.

Haka kuma taimako na da manufar ba da kwarin gwiwa ga harkokin kudi na jama'a da kawo sauye-sauye a cikin muhimman bangarorin tallalin arzikin kasar, kamar noma, makamashi, ma'adinai, sadarwa da harkokin bankuna, in ji ministan kasar.

A cewar wakilin na bankin duniya, kasar Togo tana kan hanyar fita daga mataki na farko na gyare-gyare domin shiga cikin sabon karnin samun cigaban tattalin arziki.

Sabuwar niyyar bankin duniya na bayyana yardar da hukumar take nuna wa kan karfin gwamnatin Togo na gudanar da harkokin gyare-gyaren tattalin arzikin kasar, in ji mista Herve Assad. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China