in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci Amurka da ta daina amfani da dalilan addini ta tsoma baki a harkokinta
2014-05-05 09:46:47 cri

Kasar Sin ta karyata zargin da kasar Amurka take yi mata na hana 'yancin addini, tana mai kira gare ta da ta yi watsi da wannan dalilin da take amfani da shi wajen tsoma mata baki cikin harkokin cikin gidanta.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Qin Gang ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar wa manema labarai a ranar Lahadin nan 4 ga wata, yana mai bayanin cewa, gwamnatin kasar Sin tana kare 'yancin al'ummarta na addini kamar yadda doka ta tanada, kuma al'ummar Sinawa suna walwala yadda ya kamata a karkashin ikon addini da imani kamar yadda ya kamata.

Dokar kasar Sin ba ta yarda ko wane mutum ya aikata laifi a karkashin addini ba, in ji Mr. Qin Gang.

Kwamitin kula da harkokin gida akan 'yancin addini da walwala na Amurka a rahotonsa na shekara shekara da ya fitar a ranar Jumma'ar da ta gabata ya ba da shawarar cewa, kasar ta cigaba da saka sunan kasar Sin a cikin jerin kasashen da ya kamata a damu da al'amurransu.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ya ce, tun ba yau ba bayanai dake cikin rahotan kwamitin da suka shafi kasar Sin sun kasance shaci fadi wadanda babu gaskiya a ciki, kuma ana fadin su ne da nufin karkatar da tunanin jama'a. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China