Shugaban kasar Guinea Alpha Conde zai isa birnin Washington a ranar Alhamis domin halarci wani taron yaki da cutar Ebola, bisa goron gayyatar shugaban bakin duniya Jim Kim, in ji wata majiya mai tushe. Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon, shugabar asusun IMF Christine Lagarde, shugaban bankin raya Afrika (BAD) Donald Kaberuka, shugaban kasar Saliyo Bai Koroma da kuma shugabar Liberiya Ellen Johnson-Sirleaf za su halarci wannan taron.
A watan da ya gabata, mista Conde ya yi amfani da damar da ya samu a lokacin babban taron MDD karo na 69 a New York, wajen neman taimakon gaggawa, ta yadda za'a dakatar da yaduwar cutar Ebola cikin sauri. Haka kuma ya jaddada muhimmancin karfafa tsarin kiwon lafiyar kasarsa da na ilimi, ta yadda kasar Guinea za ta samu zarafin magance duk wani nau'in cuta.
Muna bukatar taimakon kudi mai tsoka domin rage babbar asara da tattalin arzikin kasarsu ya samu, sannan da sauya salon labaran da ake watsawa dake kawo tsoro da farga ga duniya game da wannan cuta, kuma ya kamata a killace cutar Ebola ba wai kasashen ba, in ji shugaban Conde. (Maman Ada)