Kwamitin tsaron MDD ya bayyana matukar takaici game da wani harin bam, wanda ya haddasa rasuwar jami'an tawagar wanzar da zaman lafiya ta MINUSMA, 'yan kasar Chadi su 4 a arewacin Mali.
Cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a ranar Talata, daukacin wakilansa 15 sun mika sakon ta'aziyar su ga iyalai da gwamnatin kasar Chadi, bisa rasuwar ma'aikatan, tare da fatan samun sauki ga wadanda harin ya jikkata.
Kaza lika sanarwar ta bukaci mahukuntan kasar Mali da su gudanar da bincike kan wannan lamari, da nufin gurfanar da wadanda ake zargi da aikata wannan ta'asa gaban kuliya. (saminu)