Wata sanarwa da mambobin kwamitin suka bayar sun bayyana cewa, kisan ma'aikatan da ke aikin kiyayen zaman lafiya na iya zama aikata laifuffukan yaki karkashin dokokin kasa da kasa,inda suka tunatar da kungiyoyin da ke dauke da makamai da ke aikata danyen aiki a arewacin Mali kudurinsu na hada kai da majalisar dinkin duniya na ganin an dakatar da kai hare-hare kan ma'aikatan wanzar da zaman lafiya.
Don haka kwamitin sulhun ya yi kira ga gwamnatin Mali da ta yi kokarin zakulo wadanda suka kai wannan hari don ganin an hukunta su.
Alkaluman MDD na nuna cewa, tun lokacin da tawagar ta MINUSMA ta fara aiki a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2013, yawan ma'aikatan da aka kashe ya zuwa wannan lokaci ya kai 30 yayin da wasu 90 suka jikkata.
A ranar Jumma'a da safe ne dai wasu 'yan bindiga suka yiwa tawagar ta MINUSMA kwanton bauna a kan hanyar su ta zuwa yankin arewa maso gabashin kasar Mali.(Ibrahim)