in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake kwantar da wani Ba-Amurke dauke da cutar Ebola
2014-09-29 09:25:09 cri

Cibiyar binciken lafiya ta Amurka ta bayyana cewa, an kwantar da Ba-Amurke na biyar a cibiyar binciken lafiya ta kasar ta Amurka (NIH) bayan da aka gano cewa, yana dauke da cutar Ebola.

Wata sanarwa da cibiyar ta fitar ta ce, an dawo da likitan da ke aiki a wani sashe na kula da masu fama da cutar Ebola a kasar Liberia zuwa cibiyar ce, bayan da aka gano cewa ya kamu da cutar Ebola.

Ya zuwa yanzu dai Amurkawa hudu masu aikin bayar da agaji ne aka dawo da su gida daga yammacin Afirka, bayan da suka kamu da cutar Ebola, amma daya daga cikin su ya warke har ma an sallame shi daga asibiti.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ne hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, tun lokacin da cutar ta barke a yammacin Afirka ya zuwa wannan lokaci, sama da mutane 3,000 ne suka mutu yayin da aka yi imanin cewa, sama da mutane 6,500 a shiyyar sun kamu da cutar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China