Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bukaci kasashen duniya da su kara yawan adadin taimakon da suke baiwa kasashen nahiyar Afrika, musamman saboda yadda cutar Ebola mai saurin kisan bil'adama ke bazuwa a wasu kasashe dake yankin.
Wang ya yi wannan kiran ne a yayin da yake jawabi a babban taron muhawara na MDD.
Wang ya jaddada cewar, kasar Sin, a matsayinta na kawa da kuma abokiyar huldar kasashen Afrika, za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka, tare da jama'ar Afrika, kana kuma da ci gaba da tallafawa da mara wa Afrika baya iya karfinta.
Wang ya kuma shaidawa taron gagarumar rawar da Sin take takawa tare da sauran kasashen duniya wajen taimakawa Afrika tunkarar matsalar annobar Ebola. (Suwaiba)