in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Libya ta amince da sabuwar gwamnatin firaminista mai cike da rudani
2014-09-23 10:11:34 cri

A ranar Litinin din nan 23 ga wata, majalisar dokokin kasar Libya ta amince da sabuwar gwamnatin firaministan ta Abdullah Thinni wadda ta ke cike da rudani domin kawo karshen rikicin siyasar da ake fuskanta.

Kakakin majalisar Bohashim Faraj ya sanar da cewa, majalisar ta ba da amincewarta ga gwamnatin Thinni da kuri'u 110 a cikin 112 a lokacin zaman da ta yi.

Gwamnatin dai na kunshe da mukamai 13 da suka hada da mataimakin firaminista guda 3, da kuma ministoci 10, sai dai har yanzu kujerar ministan tsaro ba a cike gurbinta ba.

A wannan sabuwar gwamnati, babu ma'aikatar albarkatun mai, a cewar 'yan majalisar, wannan bangare zai koma karkashin babbar ma'aikatar mai a kasar. Tun da farko dai majalisar wakilan kasar ta yi watsi da bukatar Thinni har sau biyu ta son kafa babbar majalisar zartaswa mai dauke da ministoci 16. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China