Kungiyar dake da ra'ayin sakulanci daga Zintan mai adawa da kungiyar masu kaifin addini na kasar Libya ta kai hari na mai da martani a kan mayakan masu kaifin addini mai suna Libya Dawn a ranar Talatan nan a yammacin birnin Tripoli, kamar yadda majiyar sojin kasar ta bayyana.
Jilani Aldahish, wani kwamandan mayakan Zintan ya ce, mayakansu sun yi dauki ba dadi mai tsananin gaske tsakanin su da mayakan masu kaifin addini a yankin Wadi al-Aziziyah.
Aldahish ya ce, wannan mataki da suka dauka sun yi shi ne da nufin rage fargaba a kan Washefana, wani birni mai nisan kilomita 20 daga yammacin Tripoli, inda wata kungiyar sakulanci suke ta samu hare-hare daga kungiyar Libya Dawn mai kaifin addini.
Wadansu mazauna birnin na Tripoli sun ce, sun yi ta jin karar fashewar abubuwa masu karfin gaske, da kuma karar harbi daga motocin igwa daga tazarar mil kadan daga birnin. (Fatimah)




