A kalla mutane 150 ne aka kasha, kana wasu 100 suka jikkata a cikin wasu tashe-tashen hankali tsakanin bangarorin biyu na kabilar Mesiria dake yankin Al-Dibaib a kudu maso yammacin jihar Kordofan ta kasar Sudan, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar Sudan (SMC).
Rikicin ya barke tsakanin bangaren Awlad Omran da bangaren Al-Ziyoud na kabilar Mesiria dake yankin Al-Dibaib a cikin jihar Kordofan, in ji Mohamed Omer Al-Ansari, shugaban kabilar Mersira da kamfanin dillancin labarai na SMC ya rawaito kalamansa.
An kwashe kusan yini guda, ana tafka fada dalilin wasu gonaki dake kusa da filayen man fetur. (Maman Ada)




