Zazzabin cizon sauro na daya daga cikin cututtukan dake kashe sojojin Afrika dake cikin tawagogin wanzar da zaman lafiya, in ji janar Emmanuel Miburo, sakataren din din din a ma'aikatar tsaron kasar Burundi da tsoffin soja a ranar Litinin a birnin Bujumbura.
Birgediya janar Miburo, dake magana a yayin wani dandalin aiki karo na uku na hadin gwiwa tsakanin gabashin Afrika da yammacin Afrika kan yaki da cutar zazzabin cizon sauro a cikin jam'an tsaro, dake gudana tun daga ranar 25 zuwa 27 ga wata Agusta, inda kuma ya gayyaci shugabannin ma'aikatun kiwon lafiya dake cikin rundunonin sojojin na yankunan Afrika da su mai da hankali wajen fadakarwa kan yadda ake bincike ko gano wannan cuta a jikin 'dan adam, da kuma sanya ido kan alamun cutar da kuma yadda take yaduwa.
Zazzabin cizon sauro, cuta mai tsanani da ya kamata a hada kai da hada karfi tare domin yakar ta. Dalilin haka ne, muke nuna godiya ga kasashen yammacin Afrika da suka zo suka hade tare da mu domin hada karfin mu tare wajen yaki da wannan annoba a cikin sojojinmu, in ji janar Miburo.
Dandalin ya tattara wakilan kasashe 13 wadanda suke hada Burundi, Rwanda, Kenya, Tanzaniya, Uganda, Djibouti, Nijeriya, Nijar, Senegal, Burkina-Faso, Benin, Togo da Ghana. (Maman Ada)