Ba da jinya kan zazzabin cizon sauro mai tsanani zai zama kyauta ga yara 'yan kasa da shekaru biyar a cikin makonni masu zuwa a kasar Kamaru, inda ma irin wannan mataki tuni yake aiki ga masu fama da cutar zazzabin cizon saura tun a shekarar 2011, in ji ministan kiwon lafiya na kasar Kamaru, mista Andre Mama Fouda, a albarkacin ranar yaki da zazzabin cizon sauro ta duniya karo na bakwai da aka yi bikinta a ranar 25 ga watan Afrilu.
Kafa hanyoyin samar da magunguna sun samu bazuwa a ko'ina cikin kasar, in ji minista Mama Fouda tare da bayyana cewa, matakan da gwamnatin kasar Kamaru ta dauka a 'yan shekarun baya bayan nan sun taka muhimmiyar rawa wajen yaki da wannan cuta.
Mista Mama Fouda ya cigaba da cewa, wannan matsala ce ta kiwon lafiyar jama'a a cikin wannan kasa dake tsakiyar Afrika, yankin da ya yi karin suna kan wannan annoba.
Wadannan matakai da samar da jinya kyauta, an fara su ne a shekarar 2007, musammun ma game da ba da kulawar rigakafin wannan cuta a wajen mata masu juna biyu. (Maman Ada)